shafine da aka bude wa masoyan littatafan hausa wanda aka fi sani da hausa novel wanda ni Muhammad abba gana nake rubutawa dan wayar tare da fadakarwa ga mutane a yanayin da muke ciki.

Tuesday 21 July 2015

MUTUNTA DANGIN JUNA.

bana2.jpg

DOMIN KE DA MIJINKI
««fitowa na 4»»
ﺑﺴﻢ ﺍﻟﻠﻪ ﺍﻟﺮﺣﻤﻦ ﺍﻟﺮﺣﻴﻢ
ﻭﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻰ ﻣﺤﻤﺪ ﻭﺁﻟﻪ ﻭﺻﺤﺒﻪ ﻭﺳﻠﻢ
A duk lokacin da na wayi gari naga matata tana
matuqar qaunata tana girmamani, tana yimin
biyayya daidai gwargwadonta, toba shakka bani
da wata abokiyar rayuwa wace ta wuceta, itace
abokiyar shawarata saboda amincinta, itace
asusuna saboda amanarta.
Amma idan na wayi gari naga cewa ni kawai
takeso ba ruwanta da iyayena da 'yan uwana,
haqiqa komai nata zai fado qasa, haka zan dena
ganin girmanta kamar yadda ta dauki iyayena, ba
yadda za ayi na girmama nata, ni ta wulaqanta
nawa, halin namijin qwarai kenan a jiya da yau.
Mace itace wace kullum take fatan ganin farin
cikin maigidanta, daci gabansa, sabo da hakane
'yan uwansa suka sami albarkacinsa.
Mace ta qwarai tana son dangin mijinta yara da
manya, takanyi musu kyakkyawan zato idan
sukayi kuskure, takan taimaka musu daidai
iyawarta, ta girmamasu, ta wadata su da abinci,
da kyaututtuka, tariqa zuwa sha'anoninsu gaba
daya na haihuwa dana mutuwa, ta dage sai taga
maigidanta yana taimaka musu, wannan zaisa su
soshi sosai, itama su saki jiki da ita, har ma idan
suna neman wani abu sai kiga sun biyo ta
hannunta.
Uwarsa kuma baza taji nauyin shiga gidansa ba,
don tasan yana da mata ta qwarai.
'Yan uwansa duk zasu sota.
Da yawa zaka taras mace ta qwarai tana bawa
mijinta shawara yayiwa 'yan uwansa da
mahaifansa alkhairi, ya ziyarce su, ya tambaye su
ko suna son wani abu, ba wace take korar 'yan
uwansa tana kawo nata ba, tahana iyayensa ta
kaiwa nata, taqi girmama iyayensa tace shi kawai
take aure ba iyayensa ba.
Wannan shine sikelin da ake auna mata tagari da
matar banza.
Wannan uwace, ta haifi da da cikinta tasha
wahalar renonsa, ta qaunace shi, ta san komai na
rayuwarsa da tsaraicinsa, wannan qaunar tana
girma kamar yadda shima yakeyi.
Farat Daya sai zuciyarsa ta rabu da ita ta koma
kanki, yadena cin abincinta sai naki.
Ya dena sirri da ita saike, hatta murmushinsa da
ita ba kamar naki ba, yana yaro ne yake kwana
da ita a gado daya, yanzu sai dai ke ki shigar
dashi wani dakin kija qofa ki kulle.
Kenan kin qwace mata komai daga hannunta,
ashe wannan bai isa kiyi mata hanzari ba idan
tana cutar dake.
Idan kuma batayi ki saka mata da wahalhalunta ?
Haba 'yar uwa, Kiduba kigani, kin qwace komai
daga hannunta da mijnta da sauran 'yan uwansa
ya kamata kiyi tunani.
Duk namijin da yaga matarsa tana son iyayensa
da 'yan uwansa yakan saki jiki da ita, kuma
shima zai riqa kyautata wa mahaifanta, ya
girmama su.
Idan kuwa ta wulaqanta iyayensa da 'yan uwansa
tariqe nata, haqiqa ta janyo masa baqin jini daga
'yan uwansa.
Hatta maqwabta da sauran jama'a sun dunga
zaginsa kenan.
To ina soyayyar asalin take ?
Aure ba gidan kasuwanci bane da za a riqa
tunanin riba, aure wajen neman lahira ne ba
duniya ba, wajen neman qaunar abokin rayuwa ne
daci gabansa da daukakansa.
Sai mun hadu a darasi mai zuwa.
Insha Allah.
Share:

2 comments:

pls drop down your comment......
dan Allah ku ajiye comment.

Tallata Kayanka

Guide Tricks Blog

Be With Me Technology

Popular Posts

About Me

My photo
Hey! I’m Muhammad Abba Gana, popularly known as AbbaGana, a blog Scientist by mind and a passionate blogger by heart fountainhead of Guidetricks, Duniyan Fasaha, Duniyar Yau, Hanyantsirah, Gidan Novels, Abba Gana Novels and Be With Me Technologies, I am twenty something year old guy from Jimeta, Adamawa State, Nigeria. I’m a Freelance writer, Information marketer, professional blogger, Web designer, Internet speaker, software Developer and also an author. I make living with my laptop and can work from anywhere I find myself (as long as there is a power supply and a reliable internet connection).

Blog Archive